News
Jami’an Ƴansanda Sun Bankado Wurin Buga Jabun Kudi Na Dalar Amurka A Ondo
Rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta ce ta bankado wata masana’antar da ake zargin ana amfani da ita wajen buga jabun kuɗin dalar Amurka a ƙauyen Kiniso, da ke ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar, inda ta kama mutum ɗaya tare da ƙwato buhuna uku na kuɗin jabun dala.
Lamarin ya biyo bayan ƙorafin wani ɗan kasuwa mai suna Yusuf Nasiru, mazaunin Sabo da ke Okitipupa, wanda ya ce wasu mutane biyu sun damfare shi a cinikin canjin kuɗi.
Yan Bindiga Sun Sace Daliban Islamiyya 14 Da malamansu A Neja
A cewar ’yan sandan, mutanen sun nemi su canja dala 6,000 zuwa naira, wadda ta kai kimanin naira miliyan 8.6. Sai dai daga baya sun mayar masa da kuɗin, suna cewa ba su da isassun kuɗin naira da za su kammala cinikin.
Rahoton ya ce Nasiru ya gano cewa dalar da aka mayar masa jabun kuɗi ce, lamarin da ya sa ya kai ƙara ga ’yan sanda.
Bayan gudanar da bincike, jami’an ’yan sanda daga hedikwatar Okitipupa sun gano wani wurin da ake zargin ana buga jabun dalar a ƙauyen Kiniso, inda suka kai samame ranar 29 ga Oktoba, 2026.
A yayin samamen, sun kama mutum ɗaya, yayin da sauran mutanen da ke wurin suka tsere. Haka kuma, sun ƙwato buhuna uku na kuɗin da ake zargin jabun dala ne, tare da wasu kayayyaki da ake zargin suna da alaƙa da aikin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya ce wanda aka kama yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Felix Ohagwu, ya bayar da umarnin ƙara ƙaimi wajen bincike domin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta kuma shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan wajen hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, tare da guje wa yin mu’amala da mutanen da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News21 hours ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji

