News
Wasu Ƴan bindiga Su Yi Garkuwa Da Makafi Biyu A Filato
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutum biyu masu larurar gani, namiji da mace, a karamar hukumar Riyom ta Jihar Filato kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Shugaban ƙungiyar masu bukata ta mussaman ta kasa reshen Filato, Shindol Aaron, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce an sace mutanen ne da misalin karfe 8 na daren Litinin yayin da suke dawowa Jos daga jihar Benuwe.
Ya ce mutanen na cikin mutum tara da suka je Benuwe domin halartar wani horo, amma bayan dage taron aka umarce su da komawa Jos.
A cewarsa, mutane bakwai da ke cikin motar sun tsere, yayin da maharan suka yi awon gaba da mutum biyun.
Wani mamba a kungiyar ya bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi wasu tare da neman kudin fansa naira miliyan 50 kafin su sako wadanda suka sace.
Aaron ya ce tuni aka kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro, kuma ana kokarin ganin an kubutar da wadanda aka sace.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Filato ba ta mayar da martani kan lamarin ba.
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News16 hours ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji

