Connect with us

News

Jami’an Hisbah Sun Kama Ƴan TikTok Mata 17 A Kano

Published

on

Hukumar Hisbah Haramta Zancen Dare A Mota A Kano
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu mata matasa 17 bisa zargin yin rawa a kafar sada zumunta ta TikTok da kuma wasu da ake zargin suna yawo a wuraren da ba su dace ba a cikin birnin Kano.

An kama matan ne a wurare daban-daban, ciki har da wasu otel-otel, bisa zargin aikata abubuwan da hukumar ke ganin sun saba wa ƙa’idojin ɗabi’a.

Na Taɓa Sayar Da Manyan Makamai Ga Ƙasashe Daban-daban —Tsohon gwamnan  Abia

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Malam Mujahideen Aminuddeen, ne ya tabbatar da kamen ga jaridar Daily Trust a Kano.

Ya ce kamen wani ɓangare ne na samamen da hukumar ke ci gaba da gudanarwa domin dakile ayyukan da suka saɓa wa dokokinta da ƙa’idojin tarbiyya.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta kama wasu masu tuka babura masu kafa uku (Adaidaita Sahu) bisa zargin ɗaukar mata fasinja a gefen da direba yake zaune.

Advertisement

A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne a wurare daban-daban na jihar yayin sintiri da ayyukan sa ido da hukumar ke gudanarwa.

Mujahideen ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama ba su da cikakken ilimin addinin Musulunci, inda wasu ma ba sa iya karatu ko gudanar da ibadun yau da kullum yadda ya kamata.

Ya ce saboda haka hukumar ta fara shirye-shiryen koyar da su yadda ake alwala da sallah da sauran muhimman abubuwan addinin Musulunci.

“Mun gano cewa wasu daga cikinsu ba su da ilimin addini na asali. Muna shirye-shiryen koya musu alwala, sallah da sauran abubuwan da suka shafi ilimin Musulunci,” in ji shi.

Mataimakin kwamandan ya ƙara da cewa waɗanda aka kama za su ci gaba da kasancewa a hannun hukumar na wani lokaci domin samun karatun addini.

Ya ce manufar matakin ba hukunta su kaɗai ba ce, illa gyara halayensu da cusa musu kyawawan ɗabi’u.

Advertisement

Haka kuma, jami’in Hisbah ɗin ya jaddada aniyar hukumar na ci gaba da gudanar da aikinta na tabbatar da ɗa’a da yaƙi da munanan ɗabi’u a faɗin jihar.

Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su ƙara sanya ido kan harkokin ‘ya’yansu, musamman yadda suke amfani da kafafen sada zumunta da kuma mu’amalarsu a wuraren taruwar jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending