Connect with us

News

Na Taɓa Sayar Da Manyan Makamai Ga Ƙasashe Daban-daban —Tsohon gwamnan  Abia

Published

on

IMG 9794
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Tsohon gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce a baya ya taɓa sayar da manyan makamai ga ƙasashe daban-daban, ciki har da Libya a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar, Muammar Gaddafi.

Kalu ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce ya shiga harkar ne da nufin samun kuɗi, ba tare da la’akari da irin amfani da masu sayen makaman za su yi da su ba.

Gwamnatin Tarrayya Za Ta Fara Ba ’Yan Kasuwar Jari Bola Lasisi Domin Dakile Satar Kayayyaki

Ya ce a lokacin da yake gudanar da harkar, ba ya tantance masu sayen makaman, domin duk wanda yake da kuɗin saye zai iya samun makaman daga gare shi, ciki har da mayaƙan ƙungiyar ANC ta Afirka ta Kudu.

Sanatan ya bayyana cewa manyan makamai yake sayarwa daga wata ƙasa zuwa wata, ba ƙananan bindigogi ba. Sai dai ya ƙi bayyana inda yake samo makaman, yana mai cewa hakan sirrinsa ne.

Ya ce ya daina harkar ne bayan iyayensa sun matsa masa lamba tare da umartarsa da ya janye daga kasuwancin.

Advertisement

Kalu ya kuma tabbatar da cewa marigayi shugaban Libya, Muammar Gaddafi, na cikin waɗanda ya taɓa sayar wa makamai, inda ya yi masa addu’ar Allah ya jiƙansa.

A yayin hirar, tsohon gwamnan ya kuma yi magana kan alaƙar da ke tsakaninsa da wasu fitattun shugabannin Afirka ta Kudu, ciki har da Nelson Mandela, Thabo Mbeki, Cyril Ramaphosa da Jacob Zuma.

Ya bayyana cewa Mandela ya taɓa gaya masa cewa mahaifin Thabo Mbeki ya bayar da gudummawa mafi girma a gwagwarmayar kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu idan aka kwatanta da mahaifin Ramaphosa.

 

 

DAILY TRUST 

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending