Connect with us

News

Rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu ta kama mutum 20 kan zargin su da rura wutar zanga-zanga

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu ta kama mutum 20 wadanda ake zargin su da ruruta wutar zanga-zangar da ta mamaye sassan kasar a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Advertisement

Mutum 300 suka mace sanadiyyar yamutsin wanda ya tashi bayan an yanke wa tsohon shugaban kasar hukuncin dauri bisa laifin kin bin umurnin kotu.

Jami’an ‘yan sandan ƙasar ne suka rinƙa kai samame a larduna 6 na kasar, karkashin wani shiri na musamman da ya rinka bibiyar abubuwan da aka wallafa a shafukan sada zumunta domin zakulo wadanda suka ruruta wutar lamarin.

Advertisement

A yau Juma’a ne ake sa ran wadanda aka kaman za su gurfana a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending