News
Nijar za ta samar da sabuwar runduna a yankin Tera na jihar Tillabery
Daga Kabiru basiru fulatan
Gwamantin Nijar ta samar da bataliya ta 14 ta yankin a Téra dake jihar Tillabery , domin kara kaimi ga rundunar sojojin kasar ta Nijar, dangane da matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Sahel, musamman a yankin da ake kira da iyaka da kasashen uku.
Taron majalisar ministocin kasar ya umurci a yi amfani da wani fili da ake da shi a wani yanki da ba a gina ba mai faɗin kadada kusan ɗari (100) don soma aikin gina wannan sansani na bataliya.
A daya geffen, Shugaban kasar, Mohamed Bazoum, ya karbi bakucin babban sakatare na yankin cinikin bai daya na Afrika (ZLECAf), wato Wamkelé Mene.
Mutanen biyu sun tattauna kan taron zama na musamman na shugabannin kasashe da gwamnatoci kan ZLECAf, wanda aka shirya yi a ranar 25 ga Nuwamba, 2022 a birnin Yamai” na jamhuriyar Nijar.
