News
YANZU-YANZU: Hukumar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano Na Neman Safara’u Da Mr 442 Ruwa A Jallo
Daga Kabiru basiru fulatan
A wata tattaunawa da shugaban hukumar tace finafinai na jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallu ya yi da Sarauniya News ya bayyana cewar, yanzu haka neman Safara’u suke yi ruwa a jallo ita da mawaƙi Mr 442.

Ya ƙara da cewa yanzu haka sun arce sun yi
ƙaura daga jihar Kano, domin dokar jihar ba zata ba su damar yin abinda suke so na ɓata tarbiyya ba.
Advertisements
