News
Kanal ɗin soja ne ya ba da umarnin kashe ɗalibai a Mexico’
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wani babban jami’in gwamnatin Mexico ya bayyana cewa wani Kanal ɗin soja ne ya ba da umarnin kashe mutum shida cikin ɗalibai 43 masu koyon aikin malanta da suka ɓace a 2014 a ƙasar.
Wakilin BBC ya ce shugaban hukumar binciken laifuka ta ƙasar Alehandro Ensinas ya bayyana cewa ɗaliban shida an ajiye su ne da ransu a wani gida na aƙalla kwanaki huɗu kafin Kanal ɗin ya bayar da umarnin kashe su.
Jihar Jigawa ta cika shekaru 31 da kafuwa a matsayin jiha
A makon da ya gabata ne hukumar ta wallafa wani rahoto inda ta kira ɓacewar ɗaliban a matsayin wani laifi ga ƙasar inda ta ce akwai yiwuwar dukansu sun mutu.
Bayan wallafa rahoton ne aka bayar da umarnin kama gwamman sojoji da ƴan sanda da kuma Anthony Janar na lokacin wanda shi ne ya sa ido kan binciken ɓacewar ɗaliban.
