Connect with us

News

Dubai ta sanya wa ‘yan Najeriya sabuwar dokar shiga kasar

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADINNI

 

 

 

 

 

 

Advertisement

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta gidaya sabuwar dokar biza ga ‘yan Najeriya da ke son shiga kasar.

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita.

Nijeriya komai ya lalace a mulkin APC – Makarfi

Wannan na zuwa ne bayan da wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda ‘yan kasar ke ragaita a filin jirgin saman Dubai bayan da aka hana su shiga kasar saboda sabuwar dokar biza da Dubai ta bullo da ita.

Sanarwar ta ce ”Ofishin jakadancin Najeriya da ke Dubai ya tabbatar musu da cewa, mafiya yawan mutanen sun je kasar ne da bizar iyali, bayan da kuma suka je ba tare da kowa daga cikin iyalan nasu ba, bisa wannan dalili ne aka hana su shiga kasar, inda aka umarce su da su koma Najeriya su sake neman wata bizar, to amma wadanda suka tabbatar da cewa iyalansu na kasar an bar su sun shiga, wadanda kuma suka yi ikirarin cewa iyansu na cikin wasu jiragen da ke tafe, sai aka ce su zauna nan su jira isowar ‘yan uwan nasu”

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da sanar wa ‘yan kasar cewa Dubai ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga mutane ‘yan kasa da shekara 40, sai dai wadanda suka nemi bizar iyali.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending