Akalla mutum shida ne suka mutu a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kaddamar a kauyen Umella da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa maharan sun far wa kauyen ranar Alhamis da misalin karfe uku na rana agogon kasar, dauke da bindigogi da kuma karin wasu makaman.
Nijeriya komai ya lalace a mulkin APC – Makarfi
Jihar Benue dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya wadanda ke fama da tashe-tashen hankula da ke da alaka da ‘yan bindiga.
