News
Muna Kira A Samar Da Jami’an Tsaro Na Yankin Arewacin Nijeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Wata kungiya mai suna ‘Coalition of Northern Group’ a Turance, ta bukaci a samar da jami’an tsaro na yankin arewacin Nijeriya a kuma sa masu suna ‘Arewa Security Taskforce’, da nufin tabbatar da tsaro a fadin jihohin arewa.
Shugaban kungiyar na kasa Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi bada wannan shawara, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala taron sirri da gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, da mai ba gwamna shawara ta fannin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad a gidan gwamnati da ke Katsina.
Kwamared Charanchi, ya ce samar da hukumar tsaron ya zama wajibi, idan aka yi la’akari da yadda matsalar tsaro ke ci-gaba da yaduwa a shiyyar arewacin Nijeriya.
Ya ce shawarar samar da jami’an tsaron, wani bangare ne na shawarwarin da aka bada a cikin rahoton binciken matsalar tsaro da hanyar magancewa, wadda aka gabatar wa gwamnan a lokacin taron.
Charanci ya yaba da tabbacin da gwamnan Masari ya bada cewa a matsayin shi na shugaban kwamitin tsaro na kungiyar gwamnonin arewa zai yi nazari a kan rahoton.
