Connect with us

News

Farashin Kayayyaki Ya Yi Mummunar Tsada Irinta A Farko Cikin Shekaru 17 A Nijeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A karon farko cikin shekaru 17, tsadar farashin kayayyakin masarufi ta karu da kashi 20 da rabi 5 cikin 100 a Najeriya cikin watan Agusta da ya gabata.

Advertisement

Rabon da a ga irin wannan tashin gwauron-zabon dai tun watan Satumba na shekara ta 2005.

Federer ya sanar da yin murabus da ga wasan Tennis

Advertisement

Alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar sun nuna cewa, adadin ya karu ne daga sama da kashi 19 da aka gani a cikin watan Yuli.

Lamarin dai ya haifar da tada jijiyoyin wuya a Nijeriya, wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, yayin da babban bankin CBN ya shiga cikin matsin lambar kara kudaden ruwa.

Advertisement

Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke ci-gaba da kokawa game da halin matsin rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending