News
Mali ta gargadi ECOWAS kan tsoma baki game da batun sojojin Ivory Coast da ke hannuta
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin mulkin soji a Mali ta soki batun neman taimakon ECOWAS domin sakin sojojin kasar 49 da aka kama a Mali tun cikin watan Yuli.
A wata kakkausar suka da Malin ta yi ta ce batun sojojin abu ne da ta yi cikin doka, kuma batu ne da ya shafi kasashen biyu, dan haka ne gargadi ECOWAS da cewa ka da ta tsoma bakinta.
Gommai sun mutu a wata arangama tsakanin ISWAP da Boko Haram a Borno
sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Mali ba za ta lamunci bata suna da tursasawa ba.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da majalisar tsaron Ivory Coast ta yanke shawarar kai batun gaban kungiyar ECOWAS saboda ta shiga tsakani ta hanyar shirya zaman tattaunwa tsakanin shugabannin kasashen biyu.
Advertisements
