Connect with us

News

Kotu za ta yanke hukunci kan yajin aikin ASUU

Published

on

High court

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

A ranar Labarar nan ne ake sa ran kotun ma’aikata da ke Abuja, babban birnin Najeriya za ta yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayyar kasar ta kai kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU.

A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe wata bakwai tana yi.

Ma’aikatar kwadago ta kasar ta ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’in ta ci tura.

Gwamnati tana son kotun ma’aikatan ta bai wa mambobin ASUU umarnin su koma bakin aiki, a yayin da ake ci gaba da shari’a a kan batun.

A zamanta na farko, kotun karkashin jagorancin mai shari’a, Polycarp Hamman ta dage sauraren karar zuwa yau Laraba bayan ta saurari bayanai daga wurin masu shigar da kara da wadanda aka shigar kara.

Advertisement

Gwamnatin tarayya tana son kotun ta bayyana halasci ko haramcin yajin aikin na ASUU.

Haka kuma gwamnatin tana so kotu ta yi fashin-baki kan dokar kwadago mai sakin-layi 18 LFN 2004, musamman hukuncin yajin aiki a yayin da tattaunawa ke ci gaba tsakanin ministan kwadago da malaman jami’o’i.

Tun da fari dai, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen yajin aikin na ASUU.

ASUU ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending