News
Gwamnatin Tanzania ta haramta wa bankuna cajin kwastamomi kuɗin taransfa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙasar Tanzania ta soke kuɗin da bankuna ke cajin mutane idan suka tura kuɗi sakamakon ce-ce-ku-cen da lamarin ya jawo.
Ministan kuɗi na ƙasar Mwigulu Nchemba ya shaida wa ƴan majalisar ƙasar cewa an soke tukuicin ne bayan umarnin da shugabar ƙasar Samia Suluhu Hassan ta bayar.
Ministan ya ce wannan matakin dai zai shafi kuɗin shigar da gwamnati ke samu matuƙa, amma duk da haka an bayar da umarni ga ma’aikatu su rage kuɗin da suke kashewa wurin shirya taruka da kuma sayen kayan maƙulashe.
Tun a bara ne dai bankuna a ƙasar suka fito da wannan tsarin inda tun daga lokacin jama’a suka rinƙa ce-ce-ku-ce.
A yanzu dai wannan matakin zai kawo ƙarshen kuɗin da ake cajin kwastamomi idan sun tura kuɗi daga asusun banki zuwa ƙaramin asusu na waya, da kuma kuɗin da ake caji idan kwastamomin sun tura kuɗi tsakanin banki da banki da kuma tsakanin bankinsu da wani banki na daban.
Wannan sabon tsarin dai zai soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Okotoba.
