News
Mutane Miliyan 123 Ke Fuskantan Karancin Abinci A Nijeriya Da Wasu Kasashe – IMF
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mutane Miliyan 123 Ke Fuskantan Karancin Abinci A Nijeriya Da Wasu Kasashe – IMF
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 123 da ke kasashen Sahara Afirka ciki har da Nijeriya ke fuskantar hatsarin karancin abinci a yanzu haka.
A sanarwar da Asusun ya fitar, ya bayyana cewa sauyin yanayin da aka samu ne musabbabin karancin abinci a kasashen wanda zai shafi kokarin bunkasar tattalin arziki da kawo talauci.
Sakamakon firgicin da aka samu daga yakin Ukraine da cutar Korona sun kara hauhawar farashin kayayyakin abinci da kuma durkushewar samun kudaden shiga a daukacin Afirka wadanda suka dogara da shigowa da kayayyaki daga kasashen ketare.
IMF ya ce dukkan wadannan tashin hankali sun kara yawan mutanen da ke fama da rashin samun abinci mai gina jiki wanda suka kai na kashi 30 wato miliyan 123 a shekarar 2022 na yawan kasashen.
A cewar IMF, magance sauyin yanayi ne kadai mafita ga samun karancin abinci a Afirka, sannan akwai bukatar daukan matakai ta yadda za a shawo kan lamarin.
Sanarwar ta fitar da wasu muhimman abubawa da za a mayar da hakali a kansu kamar na habaka harkokin kasuwanci da wasu matakai da za su magance karancin abinci, kamar irin su bayar da hankali a kan tsarin harkokin kudade da inganta ababen more rayuwa da kara taimako wa talakawa da abinci da habaka harkokin noma da kuma daukan matakan shawo kan sauyin yanayi.
IMF ya kara da cewa kasashen Afirka suna bukatar karfafa kudadensu ta hanyar zuwa jari ga ‘yan kasuwa a harkokin noma tare da inganta samun riba da fadada samar da gidage ga mutanen karkara da na burane.
A cewar IMF, kasashen duniya za su taimaka musu da kudade wajen bunkasa fasahar kiomiyya.
Sauyin yanayi yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da karancin abinci a yankunan Afirka.
