Connect with us

News

Jirgin yakin Rasha ya fado kan wani gida a birnin Irkutsk

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH

Hukumomi a kasar Rasha sun ce wani jirgin yakin sojin kasar ya rikito a wata unguwa da ke kudancin Irkutsk

Jirgin yakin mai suna Sukhoi Su-30, ya fado kan wani gida mai hawa biyu a birnin Irkutsk, kamar yadda gwamnan yankin Igor Kobzev ya wallafa a shafinsa na Telegram.

Da Dumi-Dumi: Hukumar NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya Da Kasar Dubai Ta Koro

Gwamnan ya ce yana wajen da lamarin ya faru, kuma duka matukan jirgin sun mutu, amma babu wanda ya ji ciwo a cikin gidan.

Ma’aikatar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce jirgin ya rikito ne a yayin da ake kan gwajinsa.

Advertisement

Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gine-gine da dama suka kama da wuta.

Wannan dai shi ne karo na biyu da jirgi ke faduwa a kasar cikin kwanaki shida.

A ranar Litinin din da ta gabata ma wani jirgin soji ya fadi kan wani gini a kudancin birnin Yeysk, da ke kusa da kan iyaka da Ukraine, tare da kashe akalla mutum 15.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending