News
‘Yan Najeriya miliyan sama da 93 ke da damar kada kuri’a a zaɓen 2023 – INEC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar zabe ta Inec a Najeriya ta ce ‘yan kasar miliyan 93.5 ne ke da damar kada kuri’a a zabukan 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida hakan ne a Abuja a wannan Larabar a wani taro da ya gudanar da jam’iyyun siyasa.
ASUU: NLC Ta Yi Fatali Da Tsarin Gwamnati Na ‘Ba Aiki Ba Biya’
Ya ce kawo yanzu ‘yan Najeriya miliyan 12.29 ne suka kammala rajistan karbar sabbin katunan zabe, sannan bayan tantacewa sun cire sunayen mutane miliyan 2.78 daga kundinsu.
BBC ta rawaito cewa Jam’iyyun siyasar Najeriya sun nuna jindadinsu da wannan cigaba tare da fatan ‘yan kasar da ke da katunan zabe za su fita a fafata da su a babban zaben 2023.
Advertisements
