Connect with us

News

ASUU: NLC Ta Yi Fatali Da Tsarin Gwamnati Na ‘Ba Aiki Ba Biya’

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta yi fatali da tsarin nan na Gwamnatin Tarayya da take yi wa duk wata kungiyar ma’aikata barazana da shi a lokacin da ta shiga yajin aiki.

Advertisement

 

NLC dai ta yi watsi da tsarin na ‘ba aiki ba biya’ da gwamnatin ke son yin amfani da shi a kan Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta shafe watanni takwas tana yajin aiki.

Advertisement

 

Majalisar dattawa na zargin karamin ministan kwadago dakin daukar ma,aikata 77,4000

Advertisement

A baya-bayan nan ne dai ASUU ta janye tare da komawa bakin aiki bayan Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani.

 

Advertisement

Aminiya ta rawaito cewa NLC ta bukaci gwamnati ta cika dukkanin alkawuran da ta kulla da kungiyar ta ASUU gabanin komawa yajin aikin, ciki kuwa har da abin da ya shafi hakkokinsu na albashi da kuma kyautata aikinsu.

 

Advertisement

Hakan ne dai na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Shsugaban NLC, Ayuba Wabba tana mai bayyana cewa wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta saki dukkanin hakkokin malaman jami’ar a tsawon lokacin da suka dauka suna yajin aikin.

 

Advertisement

Wannan takardar dai ta fito ne bayan wani taro da Kwamitin Kolin Kungiyar ta NLC ya gudanar a Jihar Kebbi.

 

Advertisement

An shafe tsawon watanni 8 ana kai ruwa rana tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU dangane da yajin aikin gabanin cimma jituwa a makon jiya, wanda ya bayar da damar janye yajin aiki.

 

Advertisement

Sai dai Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige ya ce har sai kotu ta kammala shari’ar da ke gabanta game da yajin aikin na ASUU ne tukuna za su samu tabbacin yiwuwar biyan malaman ko akasin haka.

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending