Hadarin ya auku ne a ranar Lahadi a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal kusa da asibitin koyarwa na Jami’ar Najeriya Nsukka a Itulu-Ozalla.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa motar bas ce mai daukar mutum 14 da ta fito daga Imo zuwa Adamawa ne ta yi taho mu gama da wata tirela, inda nan take suka kama da wuta.
Masu motocin bos na haya sun fara yajin aiki a Legas
A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen Enugu, Mista Joseph Toby, ya nuna takaicinsa, inda ya ce har ya zuwa yanzu ba a gama tantance wadanda lamarin ya rutsa da su ba.
