Connect with us

News

Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya

Published

on

Yan Garkuwa da mutane

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

‘Yan bindiga na ci gaba da kai jerin hare-hare a jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina, inda suka kashe mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu jama’a domin karbar kudin fansa da kuma dabbobi masu yawa.

Rahotanni na cewa gomman mutane sun rasa ransu a cikin hare-haren da ‘yan bindigan suka kai.

Advertisement

 

Donald trump ya zargi sabuwar gwamnatin america da Bata masa suna

Advertisement

Sun kuma sace shanu a yankin gwadawaba da kauyen Kiri na yankin gada a jahar Sokoto, inda suka kashe a kalla mutane 5.

Hukumar yan sandar Najeriya a jihar ta Sokoto ta tabbatar da faruwar lamarin.

Advertisement

A jihar zamfara ma mai makwabtaka da Sokoto, ‘yan fashin dajin sun kai hari yankin nasarawar burkullu.

Wani mazaunin garin Yan Kaba na Kauran Namoda ya shaidawa BBC cewa ‘yan bindigar sun kai hari tare da kashe mutane.

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamafar ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce tuni aka kara daukar matakan tsaro da kuma dakile kai wasu hare-hare a yankin.

A yankin funtuwa ma na jahar Katsina yan bindigar sun tafi da akalla mutum 33 baya ga kashe wasu.

Advertisement

Yankin arewa maso yammacin dai Najeriya na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a daidai lokacin da aka soma yakin neman zaben 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending