Connect with us

News

Sauya fasalin naira – EFCC ta nemi taimakon bankuna da ‘yan canji don kama masu laifi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

Advertisement

 

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, EFCC, ta nemi bankuna da masu sana’ar canjin kudi a kasar su ba ta hadin kai domin kama masu laifi a harkokin kudi yayin da ake shirin sauya kudin Najeriyar.

Advertisement

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya yi kiran yayin wani taro da manyan jami’an bankuna da masu kamfanonin canjin kudi a Lagos jiya Talata.

EFCC na binciken aikin wuta na Mambila, in ji minista

Advertisement

Shugaban ya nemi bangarorin biyu da su taimaka wajen sanar da hukumar ta EFCC cikin gaggawa duk wani abu da suka gani da ya shafi alamar almundahana ko zamba musamman a wannan lokaci da kasar za ta sake sauya fasalin wasu daga cikin manyan takardun kasar.

Bawa ya bukaci bankunan da masu canjin da su sanar da hukumar tasa duk wasu bayanai masu amfani cikin gaggawa a game da ajiyar kudin da suke zargin akwai alamar rashin gaskiya da kuma sauya wa kudi ma’ajiya daga asusu zuwa wani asusun.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending