Sports
Abubuwan da za su faru a Champions League ranar Laraba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Za a kammala wasa na shida-shida a rukuni na biyar zuwa na takwas a gasar Champions League ranar Laraba kakar 2022/23.
Tuni Chelsea ta kai zagayen gaba a rukuni na biyar, Real Madrid ma mai rike da kofin bara na 14 jumulla ta kai karawar kungiyoyi16.
Masu ruwa da tsakin APC na karamar hukumar Doguwa sun ziyarci Sulen Garo
Rukuni na bakwai Manchester City ta ja ragama, sannan Dortmund ta yi ta biyu.
Rukuni na karshe na takwas Paris St Germain da Benfica sun kai bantensu, suna cikin kungiyoyin da za a raba jadawalin zagaye na biyu ranar Litinin.
Chelsea ce ta daya a rukuni na biyar da maki 10, sai AC Milan mai bakwai, sannan Salzburg mai shida da kuma Zagreb mai hudu ta karshen teburi.
Za a buga wasa tsakanin Chelsea da Dinamo Zagreb da wanda AC Milan za ta karbi bakuncin Salzburg.
Chelsea ta kai zagayen gaba a matakin mai jan ragamar rukuni na shida.
Milan za ta kai zagayen kungiyoyi16, idan ba ta bari an doke ta ba, sannan ba za ta kare a matsayi na hudu ba koda za a samu akasi.
Salzburg za ta kai zagayen gaba ne idan ta ci wasanta. Za ta yi ta hudu a rukuni idan aka doke ta, sannan Dinamo ta yi nasara.
Dinamo ba za ta kai zagayen kungiyoyi 16 ba. Za ta iya karkarewa a mataki na uku don buga Europa League amma idan ta ci wasanta, sannan sai an doke Salzburg.
Real Madrid ce ta daya a rukuni na shida da maki 10, sai RB Leipzig da tara da Shakhtar mai shida da kuma Celtic mai biyu.
Ranar ta Laraba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Celtic da wanda Leipzig za ta ziyarci Shakhtar.
Real Madrid ta kai zagayen gaba a Champions League. Za ta ci gaba da jan ragamar teburi idan ta ci wasa ko kuma aka doke Leipzig.
Leipzig za ta kai wasannin kungiyoyi 16 idan ba ta bari an doke ta ba. Za ta iya jan ragamar teburin idan ta ci wasa, sannan aka doke Real Madrid a Sifaniya.
Shakhtar za ta kai zagayen gaba ne idan har ta ci karawar da za ta yi..
Celtic za ta kammala wasa a mataki na hudu a rukuni na shida..
Manchester City ce ta daya a rukunin da maki 11, sai Borussia Dortmund ta biyu mai maki takwas, sannan Sevilla ta uku mai biyar da Copen hagen da biyu.
Manchester City za ta kara da Sevilla a Etihad ranar Laraba, sannan a kece raini tsakanin Copenhage da Dortmund.
Man City ta ja ragamar rukuni na bakwai ta kai zagayen gaba.
Dortmund ta kai zagayen gaba, bayan da ta yi ta biyu, biye da kungiyar Etihad.
Sevilla za ta kare a mataki na uku ta koma buga Europa League.
Copenhagen za ta kammala wasa a mataki na hudu a rukuni na bakwai..
Paris St Germain ta hada maki 11 a rukuni na takwas, iri daya da na Benfica, kuma dukkansu sun kai zagayen gaba.
Juventus da Maccabi Haifa kowacce tana da maki uku-uku.
Juventus za ta karbi bakuncin Paris St Germain a Italiya, sai Maccabi da Benfica da za su yi tata burza ranar Laraba.
Paris St Germain da kuma Benfica sun kai zagayen kungiyoyi 16 da za su ci gaba da wasannin – PSG ce ta daya a kan teburi mai rarar kwallo takwas, Benfiva hudu ne da ita, sannan 1-1 suka kara a tsakaninsu a cikin rukuni.
Juventus da kuma Maccabi Haifa ba za su kai zagayen gaba ba a gasar Zakarun Turai, amma dai Juventus ta uku ce a teburin.
