News
Wike ya jagoranci gwamnonin G-5 zuwa jihar Benue
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya jagoranci wasu gwamnonin Jam’iyyar PDP – da ba sa shiri da ɓangaren shugabancin jam’iyyar – zuwa jihar Benue, inda suka samu tarba daga gwamnan jihar Samuel Ortom
Sauran gwamnonin da ke cikin ƙungiyar ta G-5 sun haɗar da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
Dan takarar gwamnan jihar Kano a ADP ya taya malam Ibrahim shakarau murnar ranar haihuwar sa @67
Tuni dai waɗannan gwamnoni suka bayyana ficewa daga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, inda suka bayyana saukar shugaban jam’iyyar Iyioricha Ayu daga muƙaminsa a matsayin hanyar yin sulhu a jam’iyyar.
Advertisements
