News
Jiragen yaƙin Najeriya sun kashe wasu kwamandojin ISWAP a kusa da tafkin Chadi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce a ƙoƙarinta na kakkaɓe ragowar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas, rundunar ta ce ta ƙaddamar da wasu jerin hare-hare ta sama kan dakarun ISWAP a garin Belowa da ke yankin tafkin Chadi.
Garin na Belowa dai na daya daga cikin maɓoyar ‘yan ta’addan ISWAP da na Boko Haram a yankin tafkin Chadi.
Wike ya jagoranci gwamnonin G-5 zuwa jihar Benue
A wata sanarwa daga rundunar sojin saman, jiragen yaƙin Najeriya sun ƙaddamar da hare-haren ranar 5 ga watan Nuwamba, bayan samun bayanan sirri da ke cewa wasu shugabannin ISWAP a yankin na shirin yin wata ganawa domin shirya kai hare-hare a kan jami’an tsaro.
Daga nan ne rundunar sojin saman ta ce jami’anta suka shirya jirage domin kai farmaki, inda kuma suka tabbatar da taron mayaƙan, nan take kuma suka harba bama-bamai kansu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sa’a ɗaya bayan hare-haren ne sai jami’anta suka hangi wasu motoci biyu ɗauke da ‘yan ta’adda 13 da aka ji wa raunuka yayin harin, da niyyar kai su wata maboyar inda kuma jami’an sojin suka sake yi musu ruwan wuta.
Haka kuma BBC ta rawaito cewa rundunar sojin saman ta ce ranar 4 ga watan Nuwamba ma, jami’anta sun kai hare-hare kan ‘yan ƙungiyar ISWAP a garin Ngwuri Gan da ke ƙaramar hukumar Bama, bayan samun bayanan sirri cewa an ga mayakan cikin jerin gwanon motoci ɗauke da muggan makamai waɗanda ake zargi sun fito ne daga ƙauyukan Mina da Habuja da Kote da Tanga Lan Nga duk a ƙaramar hukumar ta Bama.
