Connect with us

News

An Gurfanar Da Wani Mutum A Kotu Kan Satar Tayar Babur

Published

on

Tayar babur

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

An gurfanar da wani mutum a gaban wata Kotun Majistare da ke zamanta Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, kan zargin satar tayar babur.

 

Advertisement

Bayanai sun ce gurfanarwar ta hada har da mai babur din da aka sace wa tayar.

 

Advertisement

Shawara ta kama ‘yan Najeriya sama da 1,600, in ji NCDC

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfeta Olumide Bamigbade, ya shaida wa kotun cewa, masu kare kansu sun aikata laifin ne ranar 6 ga Nuwamba a yankin Odo-Ado.

Advertisement

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, mai babur din ya ajiye abun hawansa ne a wajen gyara ba tare da sanin mai gyaran ba, wanda hakan ya bai wa wanda ake zargi da satar taya damar aikata laifin.

Advertisement

 

Jami’in ya kuma shaida wa kotun cewa tayar da aka sace darajarta ta kai N12,000.

Advertisement

 

Ya ce laifuffukan da aka aikata sun saba wa sassa na 261(a) da 302 na Kundin Dokokin Manyan Laifuffuka na Jihar Ekiti na 2021.

Advertisement

 

Sai dai wadanda ake tuhumar, sun musanta zargin da ake yi musu.

Advertisement

 

Lauyan masu kare kansu, Mista Femi Olarewaju, ya nemi kotun ta bai wa wadanda yake karewa beli, tare da yi wa kotun alkawarin ba za su tsere ba.

Advertisement

 

Alkalin kotun, Misis Franca Olaiya, ta ba da belin wadanda ake zargin kan kudi N100,000 ga kowannensu da kuma shaida guda-guda, kana ta dage shari’ar zuwa 24 ga Nuwamba.

Advertisement

 

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending