News
Mahaifiyar Farfesa Ibrahim Malumfashi ta rasu
Mahaifiyar Farfesa Ibrahim Malumfashi ta rasu
Allah Ya yi wa mahaifiyar fitaccen Farfesan adabin Hausa, Ibrahim Malumfashi rasuwa.
Farfesan ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Inna lillahi Wa Inna ilaihil raji’un! Yanzu Allah Ya karbi ran mahaifiyata, Fatima.”
Aminiya ta rawaito cewa Za a yi jana’izarta bayan sallar Jumu’a (1:30), a masallacin Sheikh Mahmoud Jafar da ke Unguwar Dosa, kusa da gidajen ‘yan Majalisa, Kaduna.
Advertisements
