News
Shawara ta kama ‘yan Najeriya sama da 1,600, in ji NCDC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC ta ce mutum 1,601 aka bada rahoton sun kamu da ciwon shawara a kananan hukumomi 463 da ke jihohi 36 na Najeriya da babban birnin kasar, Abuja.
An samu wannan adadi ne tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Satumban 2022.
Sudan na iya darewa’~Abdelaziz al-Hilu
A cewar rahoton, an kuma samu mutuwar mutum 15 cikin wannan adadi a jihohi 10 da ke Najeriya.
Shawara cuta ce da ake yadata ta hanyar rashi tsafta da kuma cizon sauro.
Alamominta sun hada da zazzabi mai tsanani da ciwon gabobbi da amai da gudawa.
Advertisements
