Connect with us

News

Buhari zai tafi Nijar taron ƙolin ƙasashen Afirk

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Jamhuriyar Nijar domin halartar taron ƙolin ƙasashen Afika da kuma ƙaddamar da littafi.

 

Advertisement

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya ce shugaban Buhari zai bar ƙasar ranar Litinin domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Afirka kan bunƙasa masana’antu da tattalin arziki.

‘Yan Majalisar Dokokin Nijar Sun Musanta Zargin Kara Wa Kansu Kudaden Alawus

Gabanin fara taron ƙolin shugaba Buhari zai halarci taron ƙaddamar da littafin – da Farfesa John Paden na jami’ar George Mason da ke Amurka – mai taken Muhammdu Buhari: ‘The Challenges of Leadership in Nigeria’.

Advertisement

 

Haka kuma shugaban zai halarci taro na musamman kan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge tsakanin ƙasashen Afirka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending