Connect with us

News

Mata da yara 721 aka yi wa fyade a cikin wata tara a Kano

Published

on

DAGA SHA.AIBU ABDUL.AZIZ

Hukumar kare hakkin dan adam a jihar Kano ta ce cikin watanni tara sun karbi bayanan aikata fyade har 721 daga sassan jihar.

Advertisement

Istigfari ya na janyo arziƙi da yayewar damuwa –cewar malam Mai anwaru

Shugaban hukumar ya shaida wa Jaridar Inda Ranka cewa cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA ce ta tantance tare da bin diddigin al’amarin.

Fyaɗe, matsala ce da ke ƙara ƙamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyaden.

Advertisement

Cibiyar WARAKA ta karbi korafin aikata fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata fiye da dari-bakwai, daga watan Janairu zuwa watan Satumbar shekarar nan.

Hukumar kare hakkin ɗan’adam ta jihar Kano tana aiki kafada-da-kafada da cibiyar ta WARAKA tsawon lokaci kasancewar ta mamba a kwamitin gudanarwar cibiyar.

Advertisement

Bugu-da-kari Malam Shehu ya ce kashi daya cikin uku na korafe-korafen suna gaban kotu, wasu kuma an yanke masu hukunci, amma ya ce akwai wani muhimmin aiki da cibiyar WARAKA ke tallafa wa mutanen.

Matsalar fyade ta jima tana ciwa al’umma tuwo a kwarya musamman a Najeriya, inda fyade bai tsaya a kan manya ba ko ‘yan mata, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.

Advertisement

Wasu dai na ganin rashin tsattsauran hukunci ga wadanda aka samu da laifin fyade ne yake sanya al’amarin ke kara ta’azzara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending