Connect with us

News

Boka Ya Harbe Mai Neman Maganin Bindiga Har Lahira

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Yan sanda a Jihar Enugu sun damke wani boka da ake zargi ya harbe wani da ya nemi maganin bindiga a wurinsa a yankin Karamar Hukumar Isi-Uzo.

Advertisement

 

Aminiya ta samu rahoton cewa, bokan ya harbe mutumin har lahira a lokacin da yake kokarin jarraba ingancin maganin bindigar da ya hada masa.

Advertisement

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta janye dokar hana ƴan adaidaita-sahu bin wasu tituna

 

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya bayyana a ranar Talata cewa, bokan ne ya kera bindigar da ya yi amfani da ita wajen harbe mutumin.

Advertisement

 

Binciken farko da ’yan sandan suka gudanar ya nuna bokan ya amsa cewa lallai ya yi amfani da bindiga kirar gida wajen harbin da ya yi sanadiyar mutuwar mutumin a inda yake sana’arsa ta tsubbace-tsubbace.

Advertisement

 

Bokan ya ce hakan ya faru ne lokacin da yake kokarin gwada maganin bindigar da ya hada wa marigayin.

Advertisement

 

Ndukwe ya ce batun na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar inda ake ci gaba da bincike.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending