Connect with us

News

Mahukuntan Rfi na fatan Burkina Faso ta soke matakin dakatar da Rfi a kasar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A ranar asabar Burkina Faso ta ba da umarnin dakatar da watsa shiye-shiryen gidan rediyon Faransa (RFI) nan take, bisa zarginsa da yada sakon tsoratarwa da ya shafi shugaban ‘yan ta’adda.

Advertisement

 

 

Advertisement

Ta bakin mai magana da sunan gwamnatin kasar ta haka ne RFI ta ba da gudummawa ga hanzarin kungiyoyin ‘yan ta’adda don kawar da dubban ‘yan kasar Burkina Faso da suka amince shiga aikin sa kai na kare kasar, in ji kakakin gwamnati Jean Emmanuel Ouedraogo.

Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana damuwarta kan ƙaranci man fetur a Najeriya

A farkon makon nan ne kungiyar Al-Qaeda da ke goyon bayan Musulunci da Musulmai (GSIM) a cikin wani faifan bidiyo ta yi barazanar kai hari a kauyukan da mayakan kungiyar VDP masu goyon bayan gwamnatin Burkina Faso ke karewa.

Advertisement

 

Ana baiwa masu aikin sa kai na farar hula na VDP horo na tsawon makonni biyu don yin aiki tare da sojojin da ke gudanar da ayyukan sa ido, tattara bayanai ko rakiya.

Advertisement

 

An kashe daruruwa a harin kwantan bauna da mayakan jihadi suka yi ko kuma ta hanyar bama-bamai da aka dasa a gefen titina.

Advertisement

 

Tuni dai gwamnatin kasar, a ranar asabar 3 ga watan Nuwamba, ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da abubuwan da ke cikin rahotannin gidan rediyon Faransa, in ji sanarwar gwamnatin.

Advertisement

 

“Bisa la’akari da duk abin da ya faru a baya, gwamnati ta yanke shawarar dakatar da watsa shirye-shiryen Rediyo Faransa .

Advertisement

 

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Advertisement

 

Gwamnatin kasar ta kuma zargi RFI da yada bayanan da ba su dace ba da ke nuna cewa shugaban mulkin sojan Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya ce an yi yunkurin kiffar da mulkin sa.

Advertisement

 

Kasar Burkina Faso dai ta fuskanci juyin mulkin soji sau biyu a wannan shekara, wanda jami’an soji suka fusata kan gazawar da aka yi wajen dakile barazanar kungiyoyin masu da’awar jihadi.

Advertisement

 

Wannan dai ta kasance kasa ta biyu a yammacin Afirka da ta haramtawa RFI a bana bayan kasar Mali, da ta kawo karshen watsa shirye-shiryen Rediyo Faransa na Rfi.

Advertisement

 

Shugabar Rediyo Faransa na Rfi Cecile Megie da sunan daukacin ma’aikatan Rfi ta na mai nuna goyon baya da kuma jajircewa ma’aikatan Rfi da yanzu ahak ke kawowa masu saurare labarai da suka dace cikin lokaci ba tare da nuna baganranci ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending