News
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi taro kan zaman lafiya lokacin zaben 2023
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A Najeriya, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gudanar da wani babban taron wanzar da zaman lafiya ya yin yakin neman zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe a jihar Kano.
Taron ya sami halartar shugabannin hukumomin tsaro da hukumar zabe da ƴan takarar gwamna da shugabannin jam’iyyu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Ya yin taron na Yini daya, na hadin gwiwa tsakanin rundunar ƴan sandan jihar Kano da kuma gidauniyar Aminu Magashi, an tattauna dabarun da ya kamata a yi amfani da su don tabbatar da zaman lafiya ya yin da ake tunkarar babban zaben 2023.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Mamman Dauda yace sun tsara dabarun da za su taimaka a yi zaben lafiya.
An gabatar da kasidu daban-daban game da yadda za a yi zaben lafiya daga manyan bakin da aka gayyata ciki har da hukumar zabe mai zaman kanta, inda Sulaiman Alkali jami’I a hukumar a Kano yace sabuwar dokar zaben 2022 ta sake basu kwarin gwiwa yin aiki ba sani ba sabo.
Su ma malamai sun ja kunnen ‘yan siyasa da kada su yi abin da zai haifar da fitina a cikin al’umma.
Akasarin mahalartar taron zaman lafiyar sun bukaci jami’an tsaro su yi aiki tukuru, sannan shugabanin hukumimin tsaro da suka gargadi ‘yan takara, su guji takalar junansu da kuma kaucewa yiwa juna baraza lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin zabe.
Bayanai na cewa nan gaba rundunar ‘yan sandan zata sake ganawa da ‘yan takarar a Kano don su sanya hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya.
