Connect with us

Uncategorized

Yan sandan Jihar Edo sun kashe ‘yan fashi 58, sun ceto mutum 68 a 2022

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta ce ta kama jimillar mutum 102 da take zargi da aikata garkuwa da mutane cikin shekarar 2022.

Advertisement

 

Kazalika, an ceto mutum 68 da aka yi garkuwa da su, a cewar kakakin rundunar Chidi Nwabuzor cikin wata sanarwa a yau Asabar.

Advertisement

Ni na ajiye aiki ba korata aka yi ba – Baba Impossible

Sanarwar ta ƙara da cewa dakaru sun kashe mutum 58 sannan sun kama 65 da ake zargi da aikata fashi da makami.

 

Advertisement

Haka nan, an kama wasu 64 da ake zargi da kisan kai, 193 bisa zargin shiga ƙungiyoyin asiri, da kuma 19 kan aikata fyaɗe da kuma lalata.

 

Advertisement

Cikin makaman da suka yi nasarar ƙwacewa akwai bindigogi ƙirar Ak-47, da harba-ruga 11, da ƙananan bindigogi ƙirar gida 69.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending