Connect with us

News

Hajjin 2023: Ansaka Ranar  fara jigilar maniyyatan bana  – GACA

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

Hukumar Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA), ta saki jadawalin yadda aikin jigilar maniyyata da alhazai zai kasance yayin Hajjin 2023.

 

Advertisement

Jadawalin da GACA ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa za a bude filin jirgin sama ga jirgi na farko a ranar Lahadi, 21 ga Mayu, 2023.

An ci tarar Donald Trump dala miliyan ɗaya

GACA ta ƙara da cewa za a rufe filayen jirgin saman bayan dawowar jirgin karshe wajen kammala jigilar alhazan zuwa gida a ranar Alhamis, 22 ga Yunin 2023.

 

Yayin da jigilar alhazai da ga Saudiyya zuwa gida zai fara a ran Lahadi, 2 ga Yulin 2023, sannan a kammala ran Laraba, 2 ga Agusta.

 

Kazalika, GACA ta shawarci kasashen da za su yi Hajji da su miƙa bayanan da ake buƙata daga gare su kada ya wuce ranar Litinin, 29 ga Rajab wanda ya yi daidai da 20 ga Fabrairu, 2023.

Advertisement

 

Maniyyata sama da miliyan biyu ake sa ran za su yi Hajji bana a Masarautar Saudiyya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending