Connect with us

News

NDLEA ta kama jagoran coci da wasu mutum biyu kan safarar ƙwaya

Published

on

 

 

Advertisement

 

Jami’an Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama jagoran cocin Seraphic and Sabbath Assembly da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya. tare da wasu mutum biyu bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

 

A wata sanarawa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Femi Babafemi, ya sanya wa hannu aka kuma wallafa ta a shafin hukumar na Tuwita, ta ce an kama mutanen ne bisa zargin safarar kwaya da tabar wiwi zuwa Dubai.

Advertisement

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe DPO Da Wasu ’Yan Sanda 4

Jagoran cocin mai suna Priest Nnodu Azuka Kenrick an kama shi ne bayan da ka kama wani ɗalibin kwalejin addinai ta Samanda da ke Ibadan a jihar Oyo tare da dillaliyar ƙwayar mai suna Oyoyo Mary Obasi.

 

Advertisement

Hukumar ta ce an kama mutanen ne kan yunƙurin fitar da ƙwayar ‘methamphetamine’ da tabar wiwi da aka ƙunshe cikin jarakunan manja a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke birnin Legas, domin kai su ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending