News
Buhari ya ce idanun duniya na kan jami’an tsaron ƙasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa babban sifeton ‘yan sandan ƙasar tare da manyan hafsoshin sojin ƙasar cewa idon ‘yan Najeriya da ma duniya baki ɗaya na kansu.
Yayin da ake da kyakkyawan fatan a kansu na samar da tsaron da ake buƙata domin gudanar da babban zaɓen ƙasar cikin kwanciyar hankali.
Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe kwalejojin fasaha
Shugaban ƙasar ya faɗi hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a shalkwatar tsaron ƙasar da ke Abuja, yayin ƙaddamar da kayan aikin tsaro da rundunar ‘yan sandan ƙasar ta samar.
Shugaba Buhari ya yaba wa Babban Sifeton ‘Yan sandan Ƙasar Usman Baba Alƙali game da managartan sauye-sauye da ya kawo wa rundunar ‘yan sandan ƙasar.
Buhari ya ce, “ Ya kamata na tuna muku fatana a gare ku musamman dangane da haƙƙin da ke kanku na samar da tsaro, ba iya na samar da tsaro gabanin zaɓe ba, har ma da taimakawa wajen samar da sahihin zaɓe”.
“Dangane da wannan aiki, ina kira ga Babban Sifeton ‘Yan sanda, da sauran jami’an tsaro da za su yi aiki da ‘yan sanda domin samar da tsaro a lokacin zaɓe da ku san cewa duka idanun duniya na kanku”.
Ya ƙara da cewa ”Muna aiki da tsarin dimokraɗiyya wanda dokar ƙasa ta samar, kuma duniya na yi wa ‘yan sanda kallon masu tabbatar da doka da oka a tsarin mulkin dimokradiyya”.
A ranar 25 ga watan Fabrairun da ke tafe ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokoki na ƙasa a Najeriya. Sai kuma zaɓen gwamnoni da za a gabatar ranar 11 ga watan Maris mai zuwa.
