Connect with us

News

Mun Gano ’Yan Siyasar Kano Da Ke Shirin Dauko Bakin ’Yan Daba —’Yan Sanda

Published

on

 

 

Advertisement

Yan sanda sun gano shirin wasu ’yan siyasa na dauko hayar bakin ’yan daba zuwa Jihar Kano don tayar da rikici a zaben gwamna da ’yan majalisar jiha da ke tafe ranar Asabar.

 

Advertisement

Da yake sanar da haka, kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya gargadi ’yan siyasar da ake zargi su gaggauta sanin inda dare ya yi musu domin ba su da mafaka a jihar.

Ana zargin wani dan sanda ya harbe wani mutum a Jos saboda takaddamar zaben gwamna

A cewarsa, “Ba za mu zuba ido mu kyale wasu su zo su tayar mana da hankali a jihar ba, don haka duk wanda ya tayar da tarzoma a jihar nan, za mu kama shi tare da ubangidansa mu gurfanar da sa a gaban kotu.”

Advertisement

 

Kiyawa ya jaddada cewa rundunar za ta hada gwiwa da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar da kewayenta.

Advertisement

 

Ya kuma shawarci al’umma cewa “su sa ido a yankunansu kuma su hanzarta sanar da jami’an tsaro mafi kusa a duk lokacin da suka ga wata bakuwar fuska musamman wadda ba su amince da ita ba, ta hanyar kiran wadannan lambobin waya 08032419754 ko 08123821575 ko09029292926.”

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending