News
An harbe kansila a Ebonyi
Yan sanda a Ebonyi a jiya Lahadi a Abakaliki sun tabbatar da kashe kansila, Mista Ogbonnaya Ugwu a ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Onome Onovwakpoyeya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa, an fara gudanar da bincike don gano wadanda suka kashe domin a gurfanar da su a gaban kotu.
Wani mazaunin garin ya shaida wa NAN cewa an kashe kansilan mai wakiltar Echara Ward 2 a unguwar Okposi da ke karamar hukumar Ohaozara ta Ebonyi a yayin da yake dawowa daga shagon sa.
Ita ma jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA a Ebonyi ta yi Allah wadai da kisan.
Mai magana da yawun ta, Charles Otu, ya bayyana a ranar Lahadi a Abakaliki cewa kashe-kashen da ake yi a jihar lamari ne da ke bukatar hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki.
