Connect with us

News

Yan sanda sun kama fasto kan yi wa mabiyansa fatawar yin azumin ganin Yesu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Kenya ta kama wani fasto kan zargin hannu a mutuwar mutum huɗu, sakamakon azumin da ya ce su yi don haɗuwa da Yesu.

 

Advertisement

‘Yan sanda sun ce faston mai suna Makenzie Nthenge na cikin ƙungiyar asiri a yankin Kilifi, wanda mabiyansa ke cike da burin yin azumi domin su mutu.

Alhassan Doguwa ya yi tazarce a karo na hudu

Malamin cocin dai yana shaida musu cewa hakan ce hanya mafi sauƙi ta haɗuwa da Yesu.

Advertisement

 

A yanzu dai mutum 11 ne ke karɓar magani a asibiti bayan kuɓutar da su daga inda suke ɓoye, suna azumin.

Advertisement

 

Rahotonni sun ce wasu sun yi kwana 21, ba tare da cin abinci ba, da nufin idan sun mutu za su haɗu da Yesu.

Advertisement

 

Mista Nthenge ya ce ya rufe cocin tasa tun a 2019, to sai dai ya koma amfani da shafin YouTube don yin da’awa.

Advertisement

 

A watan jiya ma, an tuhumi mista Nthenge da hannu a mutuwar wasu yara biyu, waɗanda iyayensu ke bin shafin YouTube na Mista Nthenge.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending