News
Wata ɗaliba ta ƙunnawa ɗakin kwanan ɗalibai huta a abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata ɗaliba a ɗaya daga cikin jami’o’yin dake kasar a dake Abuja, ta bunkawa ɗakin kwanan ɗalibai wuta.
Ɗalibar wacce ta tattaro katifun ɗaliban dake kwana a ɗakin da ta kunnawa wutar ta kuma samo ashana ta kunna huta akan katifun sannan ta fito wajen ɗakin ta tsaya a bakin kofa riƙe da wuƙa a hannunta.
Allah ya yiwa Ma’aikaciyar Jalla Rediyo a Kano ta rasu
Fefen bidiyan da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna yadda ɗalibar take ta murmushi a lokacin da wutar take ci ta kuma ƙi bari a shiga a kashe wutar.
Bidiyan ya nuna yadda sauran ɗaliban suke ta gudun tsira, sauran kuma na ta kururuwar kawo musu ɗauki duba da yadda hayaƙi ke tashi a sashin kwanan ɗaliban.
An jiyo wasu na mamakin wannan ɗalibar duba da yadda take murmushi da kuma kai kawo a gaban ɗakin da wutar take ci.
Wannan bidiyan dai ya samu makallata da dama, yayin da wasu suka bayyana ra’ayinsu akan cewar tabbas wannan ɗalibar tana da taɓun hankali domin ba wanda zai yi abinda ta yi cikin hankali.
Wasu kuwa na ta’allaka wannan mummunan aiki na wannan ɗalibar da cewar shaye-shaye ne ya janyo ta aikita hakan.
