News
Allah ya yiwa Ma’aikaciyar Jalla Rediyo a Kano ta rasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wayewar garin yau, Lahadi, 8/5/2023, Allah ya yi wa ɗaya daga cikin haziƙan ma’aikatan gidan rediyo na Jalla da ke Kano rasuwa.
Marigayiyar mai suna Ihsan Mukhtar Atamma ta Jalla rediyon ta rasu a yau kuma tuni an gabatar da jana’izarta da ƙarfe 10:00 na safiyar yau a unguwar Fagge, Layin marigayi Malam Mukhtar Atamma.
A madadin ma’aikatan jaridar indaranka mai albarka muna miƙa saƙon ta’aziyya ga ‘yan’uwa da iyalai da abokan aiki a Jalla Rediyo, da fatan Allah ya yi mata rahama. Amin.
Advertisements
