News
Abubuwa Sun Fashe A Kusa Da Barikin Sojoji A Abuja
Wasu abubuwa sun fashe a kusa da Barikin Sojojin Mogadishu da ke Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar.
Rundunar Sojin Nijeriya ce ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin.
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Matashin Da Ya Kone Masallata A Kano
A cewar rundunar, fashewar ta faru ne a wata ƙaramar tashar bas da ke kusa da barikin, sai dai ba ta bayar da ƙarin bayani kan abin da ya haddasa fashewar ko irin barnar da ta auku ba.
Rundunar ta ce tuni jami’anta suka fara daukar mataki domin shawo kan lamarin.
Haka kuma, Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa ta tabbatar da samun rahoton fashewar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Har yanzu ba a bayyana ko akwai wanda lamarin ya shafa kai tsaye ba, kuma hukumomi na ci gaba da bincike.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
