News
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Matashin Da Ya Kone Masallata A Kano
Babbar Kotun Shari’a da ke Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi da aka samu da laifin kunna wuta a cikin wani masallaci da ke kauyen Gadan, karamar hukumar Gezawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu.
Alkali Mai Shari’a Halhatu Huza’i Zakariyya ce ta yanke hukuncin a ranar Litinin, bayan gabatar da sahihan hujjoji da suka tabbatar da aikata laifin ba tare da tantama ba. Kotun ta tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifuka hudu masu nasaba da kisan kai da haddasa munanan raunuka.
Fusatattun Matasa Sun Cinna Wuta A Ofishin ‘Yan Sanda Na Rano
Lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayu, 2024, lokacin da wanda ake tuhumar ya kunna wuta a cikin masallacin yayin da mutane ke tsaka da ibada, abin da ya haifar da mummunan hasara ta rayuka da dukiyoyi.
Kotun ta bayyana cewa laifin ya saba wa tanadin dokar kasa, kuma laifin da ya aikata ya cancanci hukuncin kisa, domin zama izina ga wasu.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
