Connect with us

News

‘Yan sanda Sun Tabbatar Da Rasuwar DPO A Rano, Sakamakon Hatsaniyar Da Ta Faru

Published

on

IMG 20250526 WA0013

Wani lamari mai tayar da hankali ya auku a karamar hukumar Rano da ke Jihar Kano, inda aka tabbatar da mutuwar jami’in ’yan sanda mai mukamin DPO da kuma wani matashi da ke hannun ‘yan sanda, lamarin da ya janyo tarzoma da kone-kone a ofishin ‘yan sanda.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a daren Litinin, 26 ga watan Mayu, 2025.

Advertisement

Abubuwa Sun Fashe A Kusa Da Barikin Sojoji A Abuja

A cewar sanarwar, rikicin ya samo asali ne a daren Lahadi, 25 ga watan Mayu, misalin karfe 8:15 na dare, lokacin da jami’an ‘yan sanda suka kama wani matukin babur mai suna Abdullahi Musa, sakamakon korafe-korafen da al’umma suka yi kan yadda yake tuka babur cikin ganganci da kuma zargin shan kayan maye.

Bayan kama shi, Abdullahi Musa ya fara nuna alamun raunana a lokacin da yake tsare a ofishin ‘yan sanda. Lamarin da ya sa aka garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Rano, inda ya rasu da safiyar Litinin yayin da ake masa jinya.

Advertisement

Rasuwar matashin ta tayar da hankula, inda wasu bata-gari suka farmaki Ofishin ‘Yan Sanda na Rano, suka lalata wasu sassa na ofishin, suka kona motoci biyu, tare da farfasa karin motoci guda goma.

A yayin tarzomar, DPO na ofishin ya samu munanan raunuka, wanda hakan ya tilasta a garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda ya rasu daga bisani sakamakon raunukan.

Advertisement

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa tuni an kama mutane 27 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, PhD, ya kai ziyara garin Rano, inda ya duba irin barnar da aka yi, tare da kai gaisuwar ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19).

Advertisement

Haka kuma, Kwamishinan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya da adalci domin gano musabbabin tashin hankalin.

Rundunar ta bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai domin gudanar da bincike cikin nasara.

Advertisement

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sake jaddada kudirin rundunar na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da doka a fadin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending