Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Ware Kuɗi Mai Yawa Don Gyara Gadan Bayan Gobarar Masallaci

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ware kuɗi naira miliyan 151,863,895.97 domin gudanar da ayyukan more rayuwa a garin Gadan dake ƙaramar hukumar Gezawa.

Wannan na zuwa ne bayan gobarar da ta tashi a masallaci a garin a watan Mayun 2024, inda wasu mutane suka rasa rayukansu.

Advertisement

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya sanar da wannan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

‘Yan sanda Sun Tabbatar Da Rasuwar DPO A Rano, Sakamakon Hatsaniyar Da Ta Faru

A cewar sanarwar, kudin da aka ware zai taimaka wajen:

Advertisement

Gina sabon masallaci da zai maye gurbin wanda gobara ta lalata,

Gina ajujuwa biyu da ofishin malamai,

Advertisement

Gyaran bandakuna guda shida,

Samar da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, wacce za ta haɗa da babban tankin ruwa.

Advertisement

Gwamnatin jihar ta yi alkawarin ganin an kammala ayyukan cikin gaggawa don farfaɗo da rayuwar al’ummar yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending