News
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Filin Jirgin Saman Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja na wani dan lokaci sakamakon lamarin da ya rutsa da wani jirgin Max Air.
Jaridar indaranka yadda wani jirgin saman Max Air ya yi hatsari a filin jirgin Abuja da yammacin Lahadi.
Jirgin mai lamba B737 mai lamba 5N-MBD ya samu matsala a lokacin da ya sauka, kamar yadda wani bincike na farko da hukumar binciken haddurar jiragen sama a Najeriya ta fitar ya nuna.
Daily Trust ta rawaito cewa Jirgin na da fasinjoji 144 da ma’aikata shida a cikinsa. Ya kuma taso ne daga garin Yola na jihar Adamawa kan hanyar zuwa Abuja ranar Lahadi.
Sakamakon lamarin dai an karkatar da dukkan jiragen da ke kan hanyar zuwa filin jirgin na Abuja.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, yanzu jirgin na tsaye a kan titin jirgin, wanda hakan ya sa wasu jiragen ba su iya amfani da titin wajan sauka.
Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN) da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NAMA, sun tabbatar wa wakilin majiyar mu cewa, an rufe filin jirgin na dan wani lokaci har sai an dauke jirgin daga kan titun.
Da misalin karfe 7:40 na yammacin ranar Lahadi, kungiyoyin agaji na ci gaba da kokarin kau da jirgin daga wajan.
