News
Hajjin Bana: Abba Danbatta ya cefanar da kujerun da aka warewa jihar Kano – Laminu Rabi’u
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sabon shugaban Hukumar Jindadin Alhazai ta jihar Kano Alhaji Laminu Rabi’u Dan-Baffa ya bayyana takaicin yadda tsohon Shugaban Hukumar ya Siyarwa Maniyata kujeru fiye da wadanda aka Warewa jihar Kano.
Laminu Dan-Baffa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai a birnin Kano.
Ya ce an warewa jihar Kano kujeru 6,082 amma tsohon shugaban hukumar ya cefanar da kujeru 6,273 wato an sami karin kujeru 191.
“An bawa Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano kujeru 6,082 amma bisa ganganci tsohon sakataren hukumar ya sayar da kujeru 6,273, wato an sami karin dari da casain da daya (191), wanda hakan tasa dole abar wasu maniyyatan a kasa”, a cewar sabon shugaban hukuma
Advertisements
