Uncategorized
Na san ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ku – Tinubu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su ɗan ƙara sadaukarwa da kansu domin ceto ƙasar daga durƙushewa.
A cikin jawabinsa na tunawa da Ranar Dimokraɗiyya, shugaba Tinubu ya ce ya san cewa shawarar gwamnatin ƙasar ta janye tallafin man fetur, za ta haddasa ƙarin wahala ga talakawa.
Ya ce “ina jin irin raɗaɗin da kuke ji”.
Sojin Ukraine sun kwato garuruwa 3 daga hannun dakarun Rasha a kudancin kasar
Sai dai in ji shi, wannan shawara ce wadda dole ne sai an ɗauka ta domin ceto Najeriya daga durƙushewa da kuma ƙwato dukiyar ƙasar daga hannun wasu tsirarun mutane marasa kishi.
Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa haƙurinsu ba zai tafi a banza, la’akari da yarda da amanar da ‘yan ƙasar suka bai wa gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin da yake jagoranta za ta biya ‘yan Najeriya da gagarumin ƙoƙari zuba kuɗi cikin harkokin sufuri da bunƙasa da kuma samar da wutar lantarki a kai a kai baya ga ƙoƙarin bunƙasa harkokin kula da lafiya da sauran kayan amfanin al’umma.
A cewarsa sabon shugaban, gwamnatinsa za ta yi hakan ne don inganta rayuwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
Ya ce tsarin dimokraɗiyyar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Moshood Abiola ya mutu yana gwagwarmayar tabbatarwa a Najereiya shi ne wanda zai fifita da kuma kyautata jin daɗin al’umma a kan muradin ƙashin kai na shugabanni.
Da kuma tsarin da mutanen da ake mulka za su iya cimma burin rayuwarsu kuma su samu farin ciki.
Bola Ahmed Tinubu a cikin jawabin nasa ya nunar cewa shekara 30 kenan cif tun lokacin da ‘yan Najeriya suka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a 1993 don komawa ga tsarin dimokraɗiyya daga mulkin sojoji ‘yan kama-karya.
Kafin wata dokar soja ta rusa zaɓen 12 ga watan Yuni da ya bai wa Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola na jam’iyyar SDP nasara.
