News
Tankin ruwa na sama ya fado ya murkushe wani matashi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tankin sama na ruwa da ake sanya wa a gidaje ya rikito kan wani matashi wanda sanadiyar haka ya rasa ransa.
Wannan lamari dai ya faru ne a unguwar Ikotun-Ekpe da ke birnin na Ikko.
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito cew, Jamal Nureini mai shekaru 20 yana kwance ne a cikin daki a gidan su sai kawai tankin sama na ruwa na wani gida da ke makotaka da gidan su ya fado daga sama akan dakinsa da ya ke bacci, ya kuma bula kwanon dakin ya fado ya murkushe shi.
Kakar matashin Alhaja Yemisi Odejinmi wanda ta ke rayuwa da jikan nata a gidan, ta ce, wannan al’amari ya yi matukar sanya rayuwarta cikin garari.
“Ina kokarin idan Jamal ya tashi daga bacci za mu tafi fadar basaraken Legas don neman shaidar dan jiha saboda an bukaci Jamal da ya kawo a makaranta saboda ya samu gurbin karatu a jami’ar jihar Legas amma yanzu ga abin da ya faru” inji kakar marigayin
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
